Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bakin Haure Sama Da 700 Sun Mutu


This handout picture released on May 25, 2016 by the Italian Navy (Marina Militare) shows the shipwreck of an overcrowded boat of migrants off the Libyan coast today.
This handout picture released on May 25, 2016 by the Italian Navy (Marina Militare) shows the shipwreck of an overcrowded boat of migrants off the Libyan coast today.

Fiye da bakin haure 700 ne ake fargabar sun nutse a ruwa a wannan makon a wasu kwale-kwale guda uku, yayin da suke kokarin ketara tekun bahrurrum domin kaiwa ga nahiyar turai, a cewar hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya.

Akalla bakin haure 100 ne cikin wani kwale-kwalen masu safarar mutane ya nutse ranar Laraba, yayin da ba a san inda wasu mutane 550 suka shiga ba, a wani na hadari na daban da ya auku a ranar Alhamis a lokacin da kwale-kwalensu ya taso daga Libya ya nufi yankin Turai.

‘Yan sanda Italiya sun cafke matukin jirgi na biyu, wanda rahotanni suka nuna cewa dan kasar Sudan ne mai shekaru 28, bayan da wadanda suka tsira daga hadarin suka nuna shi.

Sannan har ila yau wani jirgi ya nuste a ranar Juma’a, da adadin mutanen da ba a tantance ba.

An dai ceto mutane 135, sannan an samu gawarwaki 45, amma ba a san adadin wadanda suka ba ta ba.

XS
SM
MD
LG