TARABA, NIGERIA - Yanzu haka dai ba gama sanın yawan mutanen da suka mutu ba, ciki har da mata da yara kanana da ma jarirai. Ya zuwa yanzu ana ci gaba da neman wadanda suka mutu a cikin jimlar mutane 200 da suke cikin jirgin ruwan.
Safiyanu Muhammad na daya daga cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya a hadarin jirgin ruwan. Ya ce sun shiga wani guri ne da aka tare don kamun kifi sai jirgin na su ya kasa wucewa, sai ya koma da baya har ya bugi wani itacen da aka tare ruwan da shi, kawai sai suka nutse nan take.
Alhaji jidda Sulaiman, shugaban riko na kungiyan masu kula da zirga zirgar jiragen ruwa na jihar Taraba, ya kuma tabbatar mana da faruwar lamarin amma ya ce direban jirgin ruwa ne ya dauki fasinja da yawa shi ya sa hakan ya faru.
Wani mai suna Yusuf Ali kuwa ‘yan uwansa su 12 ne a cikin jirgin amma gawa biyu kadai aka samu zuwa yanzu kuma ana kan neman sauran.
‘Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Karim Lamido, Hon. Anas Shaibu Didango, ya ce sun samu labarin nutsewar jirgin ruwan kuma bisa ga labaran, mutane sama da 40 ne suka mutu.
Yanzu haka ana kan neman sauran gawarwakinsu daga cikin ruwan, ya kuma bukaci ‘yan uwan wadanda suka rasa ransu da su yi hakuri su dauki dangana, domin za su yi dukkannin mai yiwuwa don ganin an kawo karshen yawan hadarin jirgin ruwa a wannan yankin.
SP Usman Abdullahi, kakakin rudunar ‘yan sandan jihar Taraba, ya ce kawo yanzu dai ba a samu cikakken yawan wadanda suka mutu ba sakamakon wannan hadarin jirgin ruwa.
Saurari cikakken rahoto daga Lado Salisu Garba:
Dandalin Mu Tattauna