Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Da Dama Ake Kyautata Zaton Sun Mutu Bayan Kifewar Wani Kwale-kwale A Congo


Hadarin Kwale Kwale
Hadarin Kwale Kwale

Ana kyautata zaton yawancin fasinjoji da suka kai 50 a cikin wani jirgin ruwan katako da ya kife a wani tabki a gabashin Kongo sun mutu, in ji wani jami'in yankin.

WASHINGTON, D. C. - Wani jami'in lardin Kivu ta Kudu Mustafa Mamboleo, da yake tabbatar da lamarin yace kwale-kwalen na dauke da buhuna 20 na siminti, kuma mai yiwuwa sanadiyar nutsewarsa kenan a ranar Lahadin da ta gabata, saboda yawan lodin da yake dauke da shi.

Hadarin kwale-kwale
Hadarin kwale-kwale

Ya kara da cewa mutane 10 ne suka tsira da ransu, an kuma gano gawarwaki uku, amma kuma ana ci gaba da neman mutane kusan 37.

Mummunan hadurran kwale-kwale na faruwa akai-akai a kasar Congo, inda ma'aikatan suka saba cika kananan jiragen ruwa na katako. A farkon watan Janairu, mutane 22 sun mutu a tafkin Maî-Ndombe. A watan Afrilun da ya gabata kuma mutane shida, yayin da 64 suka bace a tafkin Kivu.

Hadarin kwale-kwale
Hadarin kwale-kwale

Da yak e hira da gidan talabijin na kasar, darektan hukumar kula da Sufurin jiragen ruwa na Congo, Daniel Lwaboshi, ya ce ba a kiyaye ka'idojin ruwa sau da yawa, in da ya kara da cewa wani babban dalilin da ya sa irin wadannan hadurran ke afkuwa shine daukan kaya da mutane da ke wuce gona da iri.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG