Lamarin da ya jefa dubban mutane cikin halin rashin matsuguni.
Ruwan da aka sheka kamar da bakin kwarya daga makon karshen watan Mayu zuwa mako na biyu na watan nan na Yuni ne suka matukar haddasa barna a wasu daga cikin jihohin Nijar wace ta hada da dukiyoyi da rayukan mutane da dabbobi a cewar ma’aikatar aiyukan agajin gaggawa ta kasar wato Direction Generale de la Protection Civile DGPC.
Lamarin ya yi sandiyar rasuwar mutane a kalla 17 wadanda 6 daga cikinsu ruwa ne ya cinye su yayinda 11 kuma gidaje suka fada kansu.
Jihar Maradi ce kan gaba inda mutane 13 suka hallaka, sai Zinder 2, Tahoua 2, banda wadanda suka jikkata a jihohin Tilabery, Tahoua, Zinder da Maradi.
Ma’aikatar hasashen yanayi ta kasa wace tun a baya ta sanar cewa akwai yiyuwar samun ruwa sosai a bana, na kara tunatarwa game da haduran da damanur ta bana ka iya zuwa da su.
A sanadiyar wannan bala’i, gidaje 329 da bukkoki 111 ne suka ruguje abin da ya raba mutane 3255 da muhallansu.
Ko baya ga asarar matsugunai ma’aikatar aiyukan agajin gaggawa ta sanar cewa bisashe 325 suka mutu ta dalilin ruwan da aka tafka.
Shugaban kungiyar bunkasa aiyukan noma da kiwo ta Plate Forme Paysanne Djbo Bagna na shawartar mazauna karkara akan wasu matakan riga kafin da ya ke ganin zasu taimaka wajen takaita asara sanadiyar ambaliya.
Jamhuriyar Nijar kasar da mafi yawancin al’ummarta ke dogaro da noma da kiwo na fama da illolin canjin yanayi da a kowace shekara ke bijirowa da matsaloli kala kala.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna