Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA) tayi hasashen cewar kananan hukumomin jihar Zamfara 8 zasu fuskanci ambaliyar ruwa da bata da tsanani a daminar bana.
Babban Darkatan Hukumar NEMA, Zubaida Umar, ce ta bayyana hakan a birnin Gusau yayin wani gangamin wayar da kai akan dabarun rage karfin ambaliyar ta hanyar yin gargadi da daukar matakai da wuri.
Zubaida Umar ta zayyano sunayen kananan hukumomin da ake hasashen ambaliyar zata shafa kamar haka; Bungudu, Gumi, Gusau, Bakura, Maradun, Talatar Mafar, Shinkafi da Zurmi.
Ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya dasu yi aiki tare domin kare yankunan dake cikin hadarin ambaliya da muhimman kayayyakin more rayuwa tare da tallafawa dorewar hada-hadar tattalin arziki a fadin Najeriya, daga illolin ambaliyar ruwan.
Hasashen Hukumar Kula da Gudanawar Ruwa ta Najeriya (NIHSA) na bana ya nuna cewar jihohi 31 da kananan hukumomi 148 na cikin wuraren dake cikin matsanancin hadarin ambaliyar ruwa, yayin da jihohi 35, ciki harda Abuja, suka fada cikin wurare masu matsakaicin hadarin ambaliya, inda ake hasashen ragowar kananan hukumomi 337 su kasance cikin wurare masu karamin hatsarin ambaliya.
Dandalin Mu Tattauna