A yayin da damuna ta kan kama, Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar Yobe (YOSEMA), Dakta Mohammed Goje ya yi kira ga al’umma da su tashi tsaye su marawa gwamnati baya wajen ganin an rage barnar da ambaliyar ruwa zai iya haifar a wannan shekara ganin yadda matsalar ke zuwa kashi-kashi a jihohi daban-daban.
Dakta Goje ya bayyana hakan ne a yayın wata hira ta musamman ga Muryar Amurka a birnin tarayyar Najeriya, Abuja.
Dakta Goje ya ce ya wajabta a rika sanar da manoma da al'umma baki daya bayanan daukan matakan da suka dace da ya fito daga Hukumar Kula da Hasashen Yanayi ta Najeriya wato NiMet mai hasashe kan dükkan abubuwa da suka shafi yanayi.
Haka kuma, Dakta Goje ya ce kamata ya yi kullum gwamnati ta kasance çıkın shiri a koda yaushe don idan Abu ya bacı a san matakan da za'a dauka don samun ci gaba.
A cewar Dakta Goje ya kamata al’umma ma su tashi tsaye su tallafawa gwamnati wajen kawo bayanai da zasu taimaka a shawo kan matsalar ambaliya.
Idan ana iya tunawa, hukumar kula da hasashen yanayi ta Najeriya wato NiMet ta fitar da hasashen yanayi na shekarar 2024 a watan Febrairun, inda ta tace za’a fara damina a makare a fadin kasar.
Jinkirin daminar a shekarar 2024 a zai afku ne a wasu sassan kasar nan musamman jihohin arewa maso tsakiyar kasar, a cewar NiMet inda jihohin Borno, Abia da Akwa Ibom ne suka kasance da farkon wadanda suka ga damina.
A saurari cikakken bidiyon hirarsa da Halima Abdulra'uf:
Dandalin Mu Tattauna