Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa Ta Halaka Mutum 27 A Kamaru


Akalla mutum 27 ne suka mutu yayin da wasu fiye da 50 suka samu raunuka sakamakon ambaliyar ruwa da ta auku a Yaounde babban birnin kasar Kamaru.

YAOUNDE, CAMEROON - Hukumomin kasar ne suka sanar da hakan a ranar Litinin, yayin da masu aikin ceto suka kara zafafa neman wadanda suka bata.

Ruwan saman ya haifar da ambaliya a gundumomin Yaounde biyu a babban birnin kasar a ranar Lahadin da ta gabata, tare da share gine-gine da kuma ruguza wasu da dama.

Ma’aikatan ceto na ci gaba da tonon laka da baraguzai “da fatan ceto rayuka,” in ji Daouda Ousmanou, babban jami’in gwamnati a gundumar a ranar Litinin.

Ministan kula da yankunan Kamaru Paul Atanga Ngi, wanda ya ziyarci yankin, ya sanar da cewa adadin wadanda suka mutu ya kai 27, kuma za a yi jinyar duk wadanda suka jikkata kyauta.

"Na zo ne don mika ta'aziyyar shugaban Kamaru Paul Biya ga iyalan wadanda suka rasu," Ngi ya ce.

Masana sun danganta ambliyar da ake ganin cikin 'yan shekarun nan da matsalar sauyin yanayi.

Mummunar ambaliyar har ila yau, ta nuna tasirin matsalar gine-ginen mrasa inganci wadanda aka gina ba bisa ka’ida ba.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG