Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Mutane 45 Suka Mutu Kenya Yayin Da Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje Da Motoci


KENYA-Ambaliyar ruwa
KENYA-Ambaliyar ruwa

Ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa sun ratsa ta gidaje tare da katse wata babbar hanya a kasar Kenya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 45 tare da bacewar wasu da dama a ranar Litinin din nan, in ji ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar.

WASHINGTON, D. C. - Da farko dai jami’in ‘yan sanda Stephen Kirui ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa tsohuwar madatsar ruwa ta Kijabe da ke yankin Mai Mahiu na yankin Great Rift Valley da ke fama da ambaliyar ruwa ta ruguje, har ruwa ya shigo da laka da duwatsu da kuma bishiyu ciki.

Sai dai a wata sanarwa da ta fitar da yammacin Litinin dinnan, karamar hukumar Nakuru ta ce toshewar da wata hanyar karkashin kasa ta jirgin kasa ta yi ne ta haddasa ambaliyar ruwan.

Motoci sun makale a cikin tarkacen daya daga cikin manyan hanyoyin mota a kasar ta Kenya kuma ma'aikatan jinya sun yi jinyar wadanda suka jikkata yayin da ruwa ya mamaye manyan wurare.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta Kenya ta ce mutane 109 na kwance a asibiti yayin da wasu 49 suka bace.

Ruwan sama da ake ci gaba da yi a kasar Kenya ya haddasa ambaliya da ta kashe mutane akalla 169 tun tsakiyar watan Maris, kuma ma'aikatar hasashen yanayi ta kasar ta yi gargadin samun karin ruwan sama.

Ministan cikin gida na Kenya Kithure Kindiki ya ba da umarnin duba dukkan madatsun ruwa na jama'a da masu zaman kansu da tafkunan ruwa a cikin sa'o'i 24 daga yammacin Litinin din nan don dakile afkuwar lamarin nan gaba. Ma'aikatar ta ce za a ba da shawarwarin kwashe mutane da kuma sake tsugunar da su bayan an kammala binciken.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG