Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mummunan Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane Sama Da 70 A Tanzania Da Kenya


Tanzania - Ambaliyar Ruwa
Tanzania - Ambaliyar Ruwa

Mummunar amaliyar ruwa ta kashe mutane 58 a Tanzania cikin makonni biyu da suka gabata, a cewar gwamnatin kasar, yayin da ake ci gaba da samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar da ke gabashin Afirka.

WASHINGTON, D. C. - Ambaliyar ta fi shafar yankin na gabar teku, inda lamarin ya mutane 126,831 a cewar gwamnatin kasar.

TANZANIA
TANZANIA

Kakakin gwamnati Mobhare Matinyi ya fadi a ranar Lahadin da ta gabata cewa, an raba muhimman kayayyaki da suka hada da abinci ga wadanda abin ya shafa. Ya kara da cewa Tanzania na shirin gina madatsun ruwa guda 14 domin hana ambaliya a nan gaba.

Gabashin Afirka na fama da ruwan sama kamar da bakin kwarya, inda rahotanni suka ce an samu ambaliyar ruwa ma a makwabciyar kasar Kenya inda mutane akalla 13 suka mutu.

Reuters
Reuters

Kazalika ababen more rayuwa sun lalace, sannan an yi kira ga wadanda ke zaune a yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa da su tashi.

Ana sa ran ruwan saman zai kai kololuwar sa zuwa karshen wannan wata.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG