The country’s national disaster management office says Cyclone Gamane was projected to skim the island that sits in the Indian Ocean east of southern Africa, but changed course and made landfall in the north on Wednesday.
Ofishin kula da bala’o’i na kasar ya ce an yi hasashen cewa guguwar ta Gamane ta za ta mamaye tsibirin da ke gabar tekun India a can gefen kudancin Afirka, amma ta sauya hanya inda ta sauka a arewacin kasar ranar Laraba.
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya bayar da rahoton cewa, kimanin mutum 7,000 a tsibirin ne guguwar ta shafa. Hakan ya hada da mutum shida da suka nutse sannan wasu biyar kuma suka hallaka ta hanyar rugujewar gidaje ko fadowar bishiyoyi.
Guguwar ta yi ta yawo a hankali, yayin da ta ke ƙara ɓarnar gami da ambaliya da ta mamaye hanyoyi da gadoji da dama.
Dandalin Mu Tattauna