Ruwan samar da aka shafe sa’o’I ana yi a gundumar Kananga da ke lardin Kasai ta tsakiya, ya lalata gidaje da gien-gine da dama, gwamnan lardin, John Kabeya, ya fada yayin da ake ci gaba da kokarin ceto wadanda suka tsira.
Ya ce “an tabbatar da karin mutuwar mutane biyar daga baya a ranar Talata baya ga adadin wadanda aka ba da rahoton sun mutu da farko da su ka kai 17.
Kabeya ya ce “Rugujewar gini ya yi sanadin mutuwar mutane 10, dukkansu ‘yan gida daya ne a Bikuku.”
An samu barna sosai sakamakon ambaliyar ruwan, a cewar Nathalie Kambala, daraktar kasa ta kungiya mai zaman kanta ta Hand in Hand for Intergral Development.
Ana yawan samun ambaliya sakamakon ruwan sama mai yawa a wasu sassann kasar ta Congo, musamman ma a yankunan karkara. A watan Mayu, sama da mutane 400 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa da mamakon ruwan sama da aka yi cikin dare a lardin Kivu ta Kudu da ke gabashin Congo ya haifar.
Daga cikin gine-ginen da ambaliyar ruwan ta lalata a baya-bayan nan har da babbar cibiyar fasaha ta Congo, da majami’a da wata babbar hanya da ta katse, in ji Kabeya, wanda ya kara da cewa za’a bukaci daukar matakin gaggawa daga gwamnatin kasar.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya janyo zaftarewar kasa a gabashin Congo da yammacin ranar Lahadi, inda ya kashe mutane akalla hudu da kuma bacewar akalla mutane 20.
Dandalin Mu Tattauna