Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 120 A Kenya


Mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a Kenya ta yi sanadiyyar rasa rayuka da dama, ta kuma lakume rayukan dabbobi da rushe daruruwan gidajen jama'a.

A ranar Talata jami’ai a kasar Kenya sun bayyana cewa akalla mutane 120 ne suka mutu, iyalai daga gidaje daban-daban har 90,000 suka warwatsu sakamakon ambaliyar ruwa a kasar ta Kenya.

Kenya da makwabtanta, Somaliya da Habasha sun gamu da mummunan ambaliyar ruwa sakamakon sauyin yanayi da su ke fama da shi, wanda ake yi wa lakabi da El Nino.

Gwamnatin Somaliya ta ce, kusan mutane 100 ne suka mutu, sama da 700,000 kuma suka arce daga gidajen su akan tilas. A makwabciyar kasar Habasha kuma, a kalla mutane 43 suka rasa ransu, a cewar hukumar kula da ayukan jin kai ta MDD.

Ambaliyar ruwan ta baya bayan nan ya shafe gonakin noma da dama, tare kuma da lakume rayukan dubban dabbobi, haka kuma ta raba dubban daruruwan mutane da muhallan su.

Ambaliyar ruwan ta biyo bayan fari mafi muni da ya faru a kasar a shekaru 40, wanda ya jefa mutanen kasar da dama cikin yunwa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG