Dan wasan na kasar Masar ya zura kwallonsa ta 129 ga Reds a karawar da suka yi da Manchester United a ranar Lahadi, wanda ya kai shi ya zama dan wasan da yafi zura kwallaye a gasar Premier.
Salah ya sha gaban Robbie Fowler, wanda ya ci kwallaye 128 a gasar Premier a zaman da ya yi sau biyu a filin wasa na Anfield, inda Steven Gerrard ya ci kwallaye 120 a matsayin na uku.
Michael Owen ya ci gaba da zama a matsayi na hudu a jerin, bayan da ya zura kwallaye 118 a gasar, yayin da Sadio Mane ya ci 90 a matsayin na biyar.
Wannan gagarumar nasarar ta Salah ta zo ne yayin da ya zura wa Liverpool kwallaye biyu da suka yi nasara mai ban mamaki da ci 7-0 a kan abokanan hamayyarsu Manchester United a filin wasa na Anfield, inda ya buga wasa na 205.
Dan wasan da ke sanya lamba 11 ya fara zura kwallo ne a gasar Premier a wasan Liverpool ta buga a Watford a watan Agustan 2017 bayan ya kammala komawa kungiyar daga AS Roma a farkon kakar wasanni.
Yayin da ya fara buga wa kungiyar a kakar wasannin ta 2017-2018 ya zura jimlar kwallaye 32, inda ya lashe kyautar takalmin zinare na farko a lokuta dabab daban har sau uku zuwa yau, wanda ya hada da kakar wasanni ta 2018-2019 da kuma 2021-2022.