Cikin shekaru kusan shida da suka kwashe suna wasa tare, fitattun ‘yan wasan gaba na kungiyar Liverpool a gasar Premier League ta Ingila, Mohamed Salah da Sadio Mane, za su fuskanci juna a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka.
Senegal ta kai zagayen karshe a gasar ta AFCON bayan da ta doke Burkina Faso da ci 3-1 a zagayen semi-finals.
Egypt wacce ta yi dan taga-taga a farkon gasar, ta doke masu masaukin baki Kamaru a bugun fenariti da ci 3-1.
Wadannan sakamakon wasannin ya sa babu makawa Senegal da Egypt za su kara a wasan na karshe da za a yi filin wasa na Olembe da ke Yaounde babban birnin Kamaru.
Masu sharhi a fagen kwallon kafa da dama na kallon wannan karawa ce tsakanin Salah da Mane wadanda za su yi hamayya da juna a matakai na kasashensu.
Duka ‘yan wasan biyu zakaru ne a kungiyar Liverpool wacce ke matsayi na biyu a saman teburin gasar Premier sai dai gasar AFCON za ta raba su.
Hasali ma zuwansu gasar AFCON bai yi wa kungiyar ta Liverpool dadi ba duba da cewa gasar na gudana ne yayin da ake ganiyar fafatawa a gasar ta Premier.
Ita dai Egypt sau bakwai tana lashe kofin gasar ta AFCON, tana kuma hankoron ganin ta lashe a karo na takwas yayin da ita kuma Senegal ke kokarin ganin ta lashe kofin a karon farko.
Wannan shi ne karo na biyu a jere da Senegal ke kusantar cimma burinta na daga kofin.
A 2019 da ita aka buga wasan karshe, inda Algeria ta doke ta a kasar Egypt da ta karbi bakuncin gasar.
Wani abin mamaki shi ne, bayan wannan karawa da kasashen biyu za su yi, za kuma su sake haduwa a wata mai zuwa a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar.
Hakan ya sa wasu da dama ke ganin wannan wasan karshe na gasar AFCON da ‘yan wasan biyu za su hadu, mafari ne ga sabon babin hamayya da aka bude a tsakaninsu – akalla a matakan wadannan wasanni.
Ko da yake, bayan wadannan wasanni, ‘yan wasan biyu, wadanda rahotanni ke nuna suna da kyakkyawar alaka a kungiyarsu ta Liverpool za su mayar da takubbansu kobe don ciyar da kungiyarsu ta Anfield gaba.