Mai horar da ‘yan wasan Liverpool Jurgen Klopp, ya ce yana dari-darin yin amfani da Mohamed Salah da Virgil van Dijk da Fabinho a wasan da su buga a ranar Lahadi.
Liverpool za ta kara da Wolverhampton Wanderers a gasar Premier League a wannan karshen mako.
Klopp na nuna shakkun saka ‘yan wasan ne yayin da kungiyar ta Liverpool ke shirye-shiryen karawa da Real Madrid a wasan karshe na UEFA Champions League a ranar 28 ga watan Mayu da za a yi a birnin Paris na kasar Faransa.
A shekarar 2018, Liverpool da Real Madrid sun hadu a wasan karshe na gasar ta UEFA, inda Real Madrid ta lashe kofin.
Manajan na Liverpool ya ce “ba zai yi kasadar” saka ko daya daga cikin ‘yan wasan ba saboda wannan wasan karshe na UEFA da ke da matukar muhimmanci ga Liverpool, kamar yadda AP ya ruwaito.
Ko da yake wasan na ranar Lahadi ma na da muhimmanci ga Liverpool a gasar ta Premier, amma komai ya danganta ne ga sakamakon wasan da za a yi tsakanin Manchester City da Aston Villa a ranar Lahadi.
Idan Man City ta lashe wasanta da Aston Villa, ya zama ta lashe kofin Premier.
Idan Man City ta tashi da kunnen doki ko ta sha kaye a hannun Aston Villa, Liverpool kuma ta ci wasanta da Wolverhampton, ya zama Liverpool ce za ta lashe kofin
Idan City ta yi kunnen doki da Aston Villa, ita ma Liverpool ta yi kunnen doki da Wolves, ya zama City ce ta lashe kofin
Duk da wannan lissafi, masu sharhi dai a fagen kwallon kafa na ganin, komai yana hannun Man City a wannan lalen.