Da aka masa tambaya kan kwantaragin, sai ya ce:
"Nagode da tambayar, barka da safiya. Wannan laifina ne, na yi kuskure, na yi ma ku magana akan lamarin Mo (Salah) wanda yawanci bana yi, wanda hakan ya haifar da rashin fahimta sosai da abubuwa irin wannan. Kun sake tambaya, don haka sai na koma kan salo na baya, na sake rufe kofa. Ba ni da abin da zan ce game da duk wata kwangila ko makamancin haka, hakika ba daga wurina ba. Idan akwai wata sanarwa ku ne rukuni na farko da zai samu bayanan. Kafin nan sai dai kawai ku jira. Game da ingancin Sadio kuwa, ba lallai ne mu yi magana ba, saboda wannan abin mamaki ne."
Da aka tambayi Klopp, kocin Liverpool, “Ko shin nadin Ralf Rangnick a matsayin kocin Manchester United wata babbar nawaya ce gare shi? Sai y ace:
"Idan ka na cikin irin wannan hali za amince ne kawai cewa ka na bukatar duk wani tambari, ba za ka iya cewa kawai (sai ya danna yatsu) mu’ujizar ta faru sannan ka cigaba daga nan ba. Misali mai kyau shi ne cin 3-2 a karawa da Norwich (Manchester United ta doke Norwich City 3- 2 a Old Trafford a ranar Asabar), Ban ga cikakken wasan ba da sauran abubuwa ba da yawa amma .... Idan kun yi nasara 3-2 a gida, Premier League ne kuma dole ne ku yi nasara, babban al’amari ne, amma saboda su (Manchester United) suna cikin halin da suke ciki, dole ne ku bayyana dalilin da yasa aka tashi 3-2. Ban san ainihin yadda sakamakonmu ya kasance a kan Norwich ba, shi 3-1 ne? Saboda haka, ya dan yi kyau ne dai kawai, kuma mun yi ta fama a wasu lokutan. Sun samu yanayoyi na kwallo masu kyau kuma ku na tunanin, eh, haba fa 3-1, mance da wannan, maki uku, daga nan kwararru kan ma fara. Amma, wannan shine yanayin da suke ciki. Dole su bayyana dalilin da ya sa 3-2 ne kawai. Me yasa za ku ba su kwallaye biyu da abubuwa kamar haka. Don haka, watakila wannan shi ne bayanin, amma wannan zai kasance a duk manyan kungiyoyi a duniya."
Lallai Jurgen Klopp ya fusata da tambayoyi game da kwantaragin na Sadio Mane a jiya Litinin kuma ya shaida wa manema labarai cewa "babu abin da zai ce" game da lamarin.
Watanni 12 ne kawai su ka rage a kwantaraginsa dan wasan mai shekaru 30, wanda kwantaragin zai kare a karshen kakar wasa mai zuwa.
Dan wasan kasar Senegal da ya ci gasar AFCON ya zura kwallaye 13 a wasanni 28 a bana kuma Klopp ya dau dan wasan a matsayin dan wasa mai ban mamaki.
Klopp yana magana ne gabanin wasan EPL da kungiyarsa za ta buga da Manchester United ranar Talata, wasan da zai fafata da abokinsa Ralf Rangnick a karon farko tun lokacin Bundesliga. Rangnick da Klopp sun san juna na tsawon shekaru 15 kuma kocin na Liverpool yana tausaya wa Rangnick saboda halin da ya ke ciki a Old Trafford.