Kungiyar kwallon kafar Liverpool ta lashe gasar cin kofin FA ta bana, bayan da ta doke Chelsea a bugun fenariti, a wasan karshe ta gasar da aka fafata a yau Assabar.
Wasan na karshe dai ta karkare ne a kunnen doki ba wanda ya zura kwallo har ya zuwa karshen kayyadadden lokaci, lamarin da ya sa aka kai ga bugun penariti, inda Liverpool din ta yi galaba da ci 6-5.
Karo na 2 kenan da kungiyoyin 2 suke karawa a wasan karshe a wannan kakar wasanni, kasancewar sun hadu a watan da ya gabata a wasan karshe ta gasar League Cup, kuma kamar wasan na yau, a wancan ma ta yi galaba ne ta hanyar bugun penarity.
Wannan dai ya kara fadada mafarkin Liverpool na kafa tarihin kasancewa kungiya ta farko da ta lashe manyan gasannin kwallon kafa 4 a kakar wasanni daya a Ingila, a yayin da kuma ya disashe fatan Chelsea, wadda yanzu haka itace zakarun Turai, na karkare kakar wasanni ta bana da akalla kofi daya.
Shahararren dan wasan kungiyar Bayern Munich ta kasar Jamus Robert Lewandwoski, ya tabbatar da cewa ba zai rattaba hannun tsawaita kwantaraginsa a kungiyar ba, inda ya ce yana Muradin sauya bagire.
Daraktan kungiyar Hassan Salihamdzic, ya fada cewa Lewandowski, wanda kwantaraginsa zai karkare a watan Yuni mai zuwa, ya shaida masa aniyarsa ta barin kungiyar.
Jim kadan bayan wasan karshe da kungiyar ta buga ta gasar Bundes Liga ta bana, dan wasan ya zanta da manema labarai, inda ya ce a shirye yake ya karba duk wani tayi daga wata kungiya.
Lewandowski ya koma Bayern din ne daga Borussia Dortmund a shekarar 2014, inda kuma ya zura mata kwallaye 344, a ciki wasanni 374 da ya buga mata.
A daya bangaren kuma dan wasan kungiyar Borussia Dortmund, Erling Haaland ya zura kwallo a wasan karshe da ya buga wa kungiyar a yayin da yake ban kwana da ita, a wasan da kungiyar ta doke Hertha Berlin da ci 2-1 a yau Assabar.
Tun kafin soma wasan, sai da aka gudanar da wani kwarya-kwaryan bikin karramawa da ban kwana da dan wasan, wanda ke kan hanyarsa ta komawa Manchester City ta Ingila.
Haaland ya yi kaura ne daga kungiyar Red Bull Salburg zuwa Dortmund din a shekara ta 2020, inda kuma ya buga mata wasanni 89, daga ciki ya sami zura kwallaye 86.
Saurari rahoton Murtala Sanyinna: