Fiyeda mayakan sakai metan da hamsin daga Afghanistan dauke da bindigogi masu sarrafa kansu, da rokoki ne suka tsallaka cikin Pakistan, suka kai hari kan kauyen Bajaur.
Jami’an Pakistan sun ce maharan sun kashe akalla farar hula biyar, ciki harda mata biyu. Suka jikkata wasu mata uku a yankin kabilu dake arewa maso yammacin kasar.
Wan nan ya janyo martani daga jami’an tsaron Pakistan da wata kungiyar mayakan sakai na kabilun suka maida martani,nan da nan aka kaure da fada da ya dauki sa’o’i. Jami’an Pakistan din sun kuma bada labarin mayakan sakan sun kama suna kuma garkuwa da wasu dattijain kabilun.
Kutse da mayakan sakan suka yi yau Alhamis shine na biyu cikin wan nan wata. Mayakan sakai daga Afghnaistan sun tsallaka cikin Pakistan ranar daya ga watan nan suka kai hari kan yankin Dir mai kabilu, hakan ya janyo fada na kwana biyu da jami’an tsaro. Bayan kura ta lafa jami’an tsaro 27 da mayakan sakai 35 ne aka kashe a fadan.
Kungiyar Taliban dake Pakistan ta dauki alhakin kai wan nan hari.
Ahalin yanzu kuma mun sami labarin cewa wani bam da aka dana a gefen hanya ya tashi ya kashe mata uku da na miji daya akudancin Afghanistan.
Jami’an lardi sun ce wata motar tan-tan ce ta taka nakiyar a gundumar Maruf a lardin Kandahar jiya laraba. Fashewar ta kuma raunata wasu mutane uku.