A Yemel mayakan sakai dauke da makamai sun kai hari kan gine ginen gwamnati kusa da garin Houta, shine dai garin da suka kai ma farmaki jiya laraba.
Mazauna garin sun gayawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa, maharan a cikin wani dangajeren lokaci sun kama ofisoshin jami’an tsaro, dana masu mulki a yankin, amma daga bisani suka janye.
A jiya laraba wata kungiya da ake kira Ansar al-Shari’a, ko masu goyon bayan tafarkin shari’a, dake da alaka da kungiyar al-Qaida, sun kaiwa garin Houtan hari kamin asubahi, nan ma suka kama wasu muhimman wurare a babban birnin lardin, kuma suka ja daga da jami’an tsaro.
Ahalin yanzu kuma, kamfanin dillancin labaran Faransa ya bada rahoton cewa hukumomin Yemel sun kama mutane goma da ake zargin ‘yan al-Qaida ne.