Shugaba Barack Obama ya fadawa al’ummar Amurka cewa zai janye sojoji dubu 33 daga Afghanistan, kuma yana shirin bayyana wannan sakon ga su kansu sojojin Amurka nan gaba a yau alhamis.
Shugaban ya fadawa Muryar Amurka cikin wata hira ta musamman cewa shi da manyan mashawartansa sun yi imani da cewa hujjojin yaki su na kara gusawa, ya kuma yi alkawarin cewa ba wai Amurka zata yasar da gwamnatin Afghanistan ba ne ta hanyar janye wadannan sojoji.
A cikin hirar tasa da Muryar Amurka, Mr. Obama yace duk da janye sojoji dubu 10 da zai yi zuwa karshen wannan shekara da kuma wasu dubu 23 da zai yi cikin shekara mai zuwa, akwai sojojin Amurka da dama da zasu ci gaba da zama a can. Ya lura cewa a bayan janye wadannan sojoji, akwai sojojin Amurka dubu 68 da na kasashen NATO wadanda zasu ci gaba da kare Afghanistan yayin da ‘yan kasar suke kara daukar nauyin ayyukan tsaron kansu.
A yau alhamis Mr. Obama zai gana da sojojin runduna ta 10 ta sojojin da suka kware wajen yaki a cikin duwatsu, daya daga cikin rundunonin da aka fi yawaita tura mayakansu zuwa Afghanistan.
A halin da ake ciki, shugaba Hamidu Karzai na Afghanistan yayi marhabin da sanarwar ta shugaba Barack Obama, yana mai bayyana ta a zaman matakin da ya dace na saka ‘yan Afghanistan a kan turbar kare kasarsu. Mr. Karzai ya fada yau alhamis cewa lokaci yayi da matasan Afghanistan zasu rungumi tsaron kasar.
Shugaba Karzai yace wannan shawara ta Amurka, shawara ce da ta dace da muradun dukkan kasashen biyu.
Wata sanarwar da kungiyar Taliban ta bayar yau alhamis ta yi watsi da shawarar ta shugaba Obama a zaman ta fatar baki kawai, tana mai yin kiran da a janye dukkan sojojin NATO nan take daga kasar Afghanistan. Kungiyar ta ‘yan tsagera ta lashi takobin zafafa hare-harenta har sai lokacin da aka yi hakan.