Pakistan ta kama ‘yan kasar su biyar wadanda take zargi ‘yan tsegumi ne ga kungiyar leken asirin Amurka CIA, su take zargi da taimakawa Amurka gabannin harin da Amurkan ta kai da ya halaka Osama bin Laden.
Kafofin yada labaran kasashen yammacin Duniya sun tabbatar da labarin da jaridar New York Times ta buga, cewa kungiyar leken asirin Pakistan dake karkashin rundunar sojin kasar ta kama mutanen bayan harin da Amurka ta kai ranar 2 ga wata kan maboyar OBL a birnin Abbottabad.
Cikin wadanda hukumomin suke tsare dasu, harda wani mai mukamin manjo, wanda yake rubuta lambobin motoci dake ziyartar gidan Osam Bin Laden. Babu tabbas kan makomar mutanen.
Ahalin yanzu kuma, jami’an leken asirin Pakistan din sun bada labarin wani harin makami mai linzami da Amurka ta kai a yankin arewa maso yammacin kasar mai kabilu yak she akalla mayakan sakai su 10.
Harin da aka kai laraban nan da jiragen yakin nan da basu da matuka, an auna shi ne kan wani gidan wasu mayakan sakai, da kuma kan wata mota, kusa da garin Wana, gari mafi girma a yankin kudancin Waziristan,kusa da kan iyakar kasar da Afghanistan.