Kungiyar al-Qaida ta nada sabon shugaba, shine dan kasar Masar Ayman al-Zawahiri, ya gaji Osama bin Laden, a matsayin sabon shugban kungiyar ta ‘ta’addanci.
Kungiyar ta bada wan nan sanarwa ce a dandalin Internet na al-Qaidan. Kungiyar tayi alwashin ba zata bata lokaci ba wajen ci gaba da burinta na jihadi kan Amurka da Isra’ila, wadanda ta kira “’Yan ridda da mamaya”. Al-Qaida tace zata ci gaba da fafatawa “har sai dokacin sojojin mamayar sun janye daga kasar islama”.
Makon gobe ne al-Zawahiri, wadda likita ne zai cika shekaru sittin da haifuwa, ya juma yana na’ibin Osama bin Laden. Kwararru kan ta’addanci da jumawa suna kallon al-Zawahiri a matsayin jigon tsare tsaren kungiyar. Masu fashin baki da dama sun hakikance shi zai gaji shugabancin al-Qaida bayanda sojojin kundun balan Amurka suka kai somame a gidanda Osaman yake da zama, cikin watan jiya a Pakistan suka kashe shi.
An hakikance cewa al-Zawhiri yana tafiyar da harkokinsa ne a yankin nan mai tsaunuka kusa da kan iyakar Pakistan da Afghanistan.
Wani babban jami’in yaki da ta’addanci na Amurka John Brennan, ya fada cikin makon jiya cewa Amurka tana farautarsa.