A Yemel wasu daruruwan ‘yan bindiga ne suka kai hari kan wani gari da ake kira Houta laraba, suka kama wani sashen garin na wani dan gajeren lokaci, a fafatawa da suka yi da jami’an tsaro.
Gungun maharan da ake zargi sun kunshi ‘yan kungiyar al-Qaida, sun kaddamar da harin a goshin asubahi. Shaidun gani da ido da ma’aikatan kiwon lafiya sun ce an kashe ‘Yansanda biyu aka jikkata wasu uku a fada da aka gwabza.
Wan nan lamari ya sake tada hankali kan yiyuwar a sami karin tarzoma a kasar yayinda shuga Ali Abdullah Sale yake jinya a Saudiyya. Idan za’a iya tunawa ‘yan tawaye sun kwace wasu birane biyu a kudancin kasar.
Ahalin yanzu kuma, kafofin yada labarai anan Amurka suna cewa hukumar leken asirin Amurka tana gina wani sansani a wani wuri da ba a bayyana ba a gabas tsakiya, saboda amfani dashi wajen kai hare hare kan mayakan sakai a Yemel.