Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Pakistan Ta Musanta kama Wani Nata Domin Aiki Da Amurka

Wani dansandan a pakistan yake dagawa 'yan jarida hanu a wani wuri da aka kai harin kunar bakin wake a Islamabad.
Wani dansandan a pakistan yake dagawa 'yan jarida hanu a wani wuri da aka kai harin kunar bakin wake a Islamabad.

Rundunar sojojin Pakistan tace kariya ne tsagwara labarin cewa wai ta kama daya daga cikin hafsoshinta bisa zargin ya taimakawa Amurka wajen farauto Osama bin laden.

Rundunar sojojin Pakistan tace kariya ne tsagwara labarin cewa wai ta kama daya daga cikin hafsoshinta bisa zargin ya taimakawa Amurka wajen farauto Osama bin laden.

Kakakin rundunar mayakan kasar Manjo Janar Athar Abbas a yau laraba, ya karyata labarin da jaridar New York Times ta fara bugawa. Amma wani jami’ai na daban ya gaskanta cewa an kama wadansu mutane dangane da hari a gidan da Osama bin laden a birnin Abbottabad na Pakistan.

Wani kakakin sojojin birgediya janar Syed Azmat Ali ya gayawa MA cewa an kama mutane da dama sai dai yaki fadin laifinda ake zarginsu da shi.

Ahalin yanzu kuma jami’an aikin leken asirin Pakistan sun bada labarin cewa harin da makamai masu linzami da Amurka ta ya kashe akalla myakan sakai goma sha biyar a yankin arewa maso yammacin kasar mai kabilu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG