Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matashi ‘Dan Shekara 17 Ya Kashe Wani Dalibi A Makarantar Jihar Iowa


Police respond to a shooting at Perry High School in Perry, Iowa, Jan. 4, 2024. Police said a 17-year-old student killed one child and wounded five other people.
Police respond to a shooting at Perry High School in Perry, Iowa, Jan. 4, 2024. Police said a 17-year-old student killed one child and wounded five other people.

Wani matashi dan shekara 17 ya bude wuta a wata karamar makarantar sakandare ta Iowa a Amurka, a rana ta farkon komawa makaranta bayan hutun hunturu, inda ya kashe wata yarinya ‘yar aji shida tare da raunata wasu biyar a ranar Alhamis yayin da daliban suka yi shinge a ofisoshi a firgice.

WASHINGTON, D. C. - Wanda ake zargin, dalibi ne a makarantar da ke Perry, ya mutu sakamakon abin da masu bincike suka yi imani da cewa harbin bindiga ne da ya yiwa kansa, in ji wani jami’in binciken manyan laifuka na Iowa.

Hukumomi sun ce daya daga cikin mutane biyar da suka jikkata wani jami'in gwamnati ne, sannan daga bisani aka bayyana sunan sa cewa shugaban makarantar Perry ne, Dan Marburger.

Hukumomi sun bayyana cewa, sunan maharbin Dylan Butler, mai shekaru 17, amma kuma ba su bayar da wani bayani ba game da dalilin bude wutar.

Mitch Mortvedt, mataimakin daraktan sashen bincike na jihar, ya ce ana binciken dalilin harbin da ake zargin, kuma hukumomi na duba "yawan rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta" da ya yi kafin lokacin harbin, Mortvedt ya kara da cewa, dukkan harbe-harbe sun faru ne a cikin makarantar sakandaren, amma ya ce wasu dalibai daga wasu azuzuwa na iya kasancewa a wurin don lokacin shirin kumallo ne.

An shirya gangamin bankwana ranar Alhamis da yamma a wurin shakatawa da cocin garin. Gwamna Kim Reynolds ya ba da umarnin a sauke dukkan tutoci a Iowa zuwa rabin maki nan da nan a ranar Alhamis kuma su kasance a rabin maki har sai faduwar rana a ranar Lahadi, don tallafawa da jaje ga al'umma da daliban makarantar, iyalai, da malamai.

A birnin gundumar Washington, an yi wa babban mai shigar da kara na Amurka Merrick Garland bayani kan harbin. Jami'an FBI daga ofishin Omaha-Des Moines suna taimakawa a binciken da sashin binciken laifuka na Iowa ke jagoranta.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG