Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Goyi Bayan Malaman Makarantu Su Dinga Rike Bindigogi


Shugaba Trump da wasu daga makarantar da aka kashe mutane 17 makon jiya
Shugaba Trump da wasu daga makarantar da aka kashe mutane 17 makon jiya

Biyo bayan harin da aka kai wata makaranta a Florida makon jiya, shugaban Amurka ya goyi bayan malamai su dinga zuwa makaranta da bindigogi domin su kare kansu amma da alama hakan bai samu karbuwar mutanen da suke tare da shi ba

Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna goyon bayan samarwa malamai makamai, yayinda yake musayar miyau da daliban da kuma iyayen ‘yaran makarantar da aka kai harin kan mai uwa da wabi.

Shugaba Trump ya kuma fada yayinda yake tattaunawa dasu a dakin cin abinci na fadar White House cewa, “A kuma baza tsofaffin sojoji a ko’ina cikin makaranta. Zamu yi nazari a kan wannan sosai.”

A wani lokaci Trump ya yi tambaya cewa, Akwai wanda ya goyi bayan wannan shawarar?”

Mutane kalilan suka daga hannunsu. Daga nan sai ya yi tambaya cewa, wanene bai goyi baya ba, sai mutane da dama suka daga hannu daga cikin kimanin mutane arba’in da suke dakin da suka hada da dalibai dake dingishi da kuma malaman makarantar da aka yiwa harbin.

Trump ya kuma yi kira da a janye dokar hana daukar bindiga kusa da makarantu, yace gwamnatinsa zata kara maida hankali wajen yin cikakken bincike kafin a sayarwa mutum da bindiga, za a kuma kara shekarun mallakar bindiga. A halin yanzu jihohi ishirin da takwas na Amurka, basu kayyade shekarun mallakar bindiga ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG