Hukumomin tsaro a jihar Texas da ke kudu maso yammacin Amurka, na fuskantar zafafan tambayoyi kan tsawon lokacin da suka kwashe kafin su kai dauki a makarantar da wani dan bindiga ya harbe yara 19 da malamai biyu har lahira a wannan mako.
Jami’ai sun ce dan bindigar mai suna Salvador Ramos mai shekaru 18, wanda ya daina zuwa makaranta, ya kwashe minti 40 zuwa sa’a daya yana cin karensa ba babbaka a makarantar.
Sai daga bisani ‘yan sanda suka kutsa wani aji hudu na firaimare, inda ya riga ya kashe mutum 21 a makarantar da ake kira Robb Elementary School da ke garin Uvalde a jihar ta Texas.
Wadanda suka shaida lamarin sun ce iyayen yaran da dan bindigar ya rutsa da su a makarantar, sun yi ta yi wa ‘yan sandan ihu da su kutsa cikin makarantar a lokacin harbin wanda ya auku a ranar Talata, amma hakan ya ci tura.
Su dai ‘yan sanda sun ce ba su da masaniya kan iya tsawon lokacin da dan bindigar ya kwashe a cikin ginin makarantar.
Gabanin hakan, gwamnan jihar Greg Abott, ya dora alhakin abin da ya faru akan matsaloli na lafiyar kwakwalwa da suka damu matashin dan bindigar.