Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk Makarantun Sakandaren Amurka Zasu Yi Gangami Yau Laraba


Wasu 'yan makaranta da malaman makarantar Florida inda aka kashe mutane 17 watan jiya
Wasu 'yan makaranta da malaman makarantar Florida inda aka kashe mutane 17 watan jiya

A yunkurin tabbatar cewa an daina kashe kashe a makarantu duk ilahirin makarantun sakandare dake Amura zasu yi gangami na mintuna 17 domin tunawa da mutane 17 da aka kashe a jihar Florida

Yau za a gudanar da wani gangami a duk fadin Amurka da ya shafi ‘yan makaranta da malamai da kuma iyaye, da “taken ya isa haka”.

Za a gudanar da gangamin ne daidai ranar da aka cika wata guda da harbin kan mai uwa da wabi da aka yi a wata makarantar sakandare ta jihar Florida inda aka kashe mutane goma sha bakwai.

Wata kungiyar matasa ce ta shirya gangamin tare da hadin gwuiwar wata kungiyar mata dake fafatukar inganta rayuwar matasa. Za a fara gangamin ne a daidai karfe goma na safe agogon sassan kasar na tsawon mintoci goma sha bakwai domin tunawa da mutane 17 da aka kashe a makarantar sakandare ta Marjory Stoneman Douglas High School a Parkland a Florida, ranar sha hudu ga watan Fabrairu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG