Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Da Aka Kai Hari Makarantarsu A Jihar Florida Sun Koma Makarantar


Daliban makarantar Stoneman Douglas dake Florida
Daliban makarantar Stoneman Douglas dake Florida

Bayan an rufeta na tsawon makonni biyu saboda mummunan harin da aka kai makarantar da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 17, jiya daliban da suka tsallake rijiya da baya suka koma karatu a makarantar.

Daliban da suka tsallake rijiya da baya a harbin kan mai uwa da wabin da ya kasance daya daga cikin harin da aka yi asarar rayuka da dama a tarihin Amurka sun koma makaranta jiya Laraba, yayinda 'yan majalisun jiha da na tarayya suke muhawa kan yadda za a shawo kan asarar rayukan matasa a makarantu.

An rufe makarantar Stoneman Douglas dake jihar Florida tunda mahari ya kashe mutane goma sha bakwai a makarantar makonni biyu da suka shige.

Kisan da aka yi a makarantar ya sake tada muhawara kan dokokin mallakar bindiga, inda 'yan makarantar sakandare da dama suka shiga gangamin neman kafa dokar mallakar bindiga.

Daliba Nicole Gonzales tace komawa cikin makarantar ba abu ne mai sauki ba.

Ta ce “Ban yi tsammani akwai wanda yake ji a jika ko kuma a tunanensa ya yi shirin shiga kofar makarantar ba”.

Harin ya sa majalisar dokokin jihar Florida yin muhawara kan batun kare dalibai a makarantu.

A majalisar wakilai, kakakinta Paul Ryan ya shaidawa manema labarai ranar Talata cewa, tilas ne a cike gibin dake akwai kan binciken da ake gudanarwa akan masu neman sayen bindiga.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG