Iran ta yi fatali da jan kunnen da Amurka ta yi mata akan toshe mashigin nan na Hormuz da jiragen dake jigilar man fetur suke bi ta cikinsa suna ratsawa, wanda a kansa ne gardama ta kaure tsakanin kasashen biyu.
A yau Alhamis ne cibiyar labaran gwamnati ta Fars take ruwaito kwamandan mayakan juyin juya-halin Iran Hosseini Salami yana cewa, Iran na iya tsara abinda ya kira “matakan kanta na tsaron kanta.”
A farkon makon nan ne Iran ta yi barazanar zata toshe wannan mashigin na Tekun Pasha muddin kasashen Yamamcin Turai suka ce zasu kara zafafa matakan karya tatalin arzikin Iranm da suke dauka.
Karin wadanan matakan zasu dada saka Iran a cikin mawuyacin hali tunda zasu kasance kari ne bisa matakan takunkumi masu yawa da daman kasashen suka dauka kanta a dalilin zargin da suke wa Iran na cewa tana kokarin kera makaman nukiliya.
Fiye da sulusi daya na dukkan man da ake jigila ta jiragen ruwa, ta wannan mashigin na Hormuz yake ratsawa, saboda haka duk wata tsohewar da za’a yi wa hanyar, zai janyo matsaloli barkattai ga sha’nin man fetur a duniyar ma baki dayanta