Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A sa'ilinda zanga-zanga ke wanzuwa, dakarun Sham sun hallaka mutane 24


Gobarar da ta tashi a matatar man Homs kenan sanadiyyar tashe-tashen hankula
Gobarar da ta tashi a matatar man Homs kenan sanadiyyar tashe-tashen hankula

‘Yan gwagwarmaya a Siriya ko Sham sun ce jami’an tsaro sun kashe a kalla mutane 24,

‘Yan gwagwarmaya a Syria ko Sham sun ce jami’an tsaro sun kashe a kalla mutane 24, ciki har da yara da dama, a yayin da zanga-zangar kyamar manufofin gwamnati ke ta yaduwa a fadin kasar.

Wata kungiyar rajin kare hakkin dan adam Sham mai hedikwata a Burtaniya ta gaya ma Muryar Amurka cewa jiya Jumma’a an bindige wasu yara kanana uku ‘yan shekaru 10 da 12 da 14 har lahira a ciki da kewayen birnin Homs mai fama da tashin hankali. Haka zalika an bindige wata yarinya ‘yar shekaru 12 a kudancin kasar.

Duk ko da kara munin da tashin hankalin ke yi ‘yan Sham sun bazu bisa tituna suna gangamin goyon bayan abin da su ka kira zanga-zangar tsira da mutunci. ‘Yan gwagwarmaya su ka ce zanga-zanga mafi girma da kuma mafi yawan tashin hankalin sun fi aukuwa ne a birnin Homs, inda nan ne aka cika amfani da munanan hanyoyin murkushe zanga-zangar. Ita ma Majalisar ‘Yan Kishin Kasar Sham ta bayar da wata sanarwa inda ta yi gargadin cewa wani mummun kashe-kashe na tafe a daidai lokacin da jami’an tsaron gwamnati ke zagaye da birnin Homs.

Haka zalika an yi zanga-zanga a birnin Daraa na kudancin kasar, da kuma birnin Idlib na arewa maso yammacin kasar a kusa da kan iyakar Sham da Turkiyya, da kuma Deir el-Zour da ke gabashin kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an hallaka akalla mutane 4,000 tun bayan da tashin hankalin ya barke a watan Maris, kuma Sakatare-Janar na Majalisar Ban ki-moon ya sake maimaita wannan adadin a jiya Jumma’a, ya ce wannan adadin mutanen da su ka mutu da MDD ta bayyana an samu ne daga ingantattun kafofi.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG