Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MASAURATAR KANO: Gwamnati Ta Haramta Zanga-zanga a Jihar


Gwamna Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)
Gwamna Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya haramta duk wata zanga-zanga tare da kama duk wani dalibi da ke shirin tada zaune-tsaye a jihar yayin da ake ci gaba da tirka-tirka tsakanin sarakunan Kano biyu wato Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.

Gwamnan ya yi ikirarin cewa ‘yan jam’iyyar adawa na yunkurin daukar nauyin wasu dalibai daga wasu jihohi don tayar da hankali a jihar, kamar yadda mai magana da yawunsa Sanusi Bature ya bayyana cikin wata sanarwa a yau Laraba.

“Gwamnan ya bai wa ‘yansanda, da ‘yansandan farin kaya, da jami’an tsaron Civil Defence umarnin kamawa da tsarewa da tuhumar duk wani mutum ko kungiya da suka shiga zanga-zanga a kan titunan Kano,” in ji sanarwar.

Gwamnan ya gargadi kungiyoyin dalibai da su guji kawo rikici a Jihar Kano.

Gwamna Yusuf, ya bukaci ‘yan jihar da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum kamar yadda suka saba, yayin da gwamnati ke kokarin wanzar da zaman lafiya.

Ya kuma jaddada cewa gwamnati na ci gaba da taka-tsan-tsan, kuma a shirye ta ke ta dakile duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya a Kano.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG