Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masari Ya Mai Da Martani Akan Haramta Yawon Kiwo A Jihohin Kudu


KATSINA: Gwamnan Katsina Bello Masari
KATSINA: Gwamnan Katsina Bello Masari

Gwamnan Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ya bayyana cewa, yawon kiwo ya sabawa koyarwar addinin makiyaya wadanda akasarinsu musulmai ne, haka kuma cigaba da yin haka ba shi ne mafi a’ala ga warware yawan rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya a fadin Najeriya ba.

Tun bayan da gwamnonin kudancin Najeriya suka haramta yawon kiwo a jihohinsu a wani taro da suka gudanar a Asaba ta jihar Delta, ake ci gaba da tafka muhawara tare da samun martani daga kusan duk sassan kasar.

Da alama kuma matakin na gwamnonin na kudu, ya sami amincewa da goyon bayan wasu shugabanni da masu fashin baki a Arewacin Najeriya.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari na cikin masu wannan ra'ayin, na rashin goyon bayan yawon kiwo barkatai.

A yayin da yake jawabi a wani bikin cikarsa shekara biyu a wa’adin mulkinsa na biyu, Masari ya ce yawon kiwo barkatai na daga cikin matsalolin da ake fuskanta wanda ya ki ci ya ki cinyewa a yanzu inda ya ce a matsayin sa na gwamna ba ya goyon bayan a ci gaba da kiwo ta wannan hanyar.

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbanjo A Katsina Yayinda Yaje Jaje Kan Iftila'in Ambaliyar Da Ya Auku
Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbanjo A Katsina Yayinda Yaje Jaje Kan Iftila'in Ambaliyar Da Ya Auku

To sai dai kuma gwamnan ya jaddada muhimmancin samar da wadatattun abubuwan da ake bukata kamar wuraren kiwo na zamani da dai sauran su domin hana yawon kiwo daga wani yanki zuwa wani da sunan neman abincin dabbobi.

Masari ya ce neman ruwa da ciyawa ne dalilin da ya sa makiyaya ke tashi su je wani wuri, kuma idan gwamnati ta samar da su, ba abin da zai sa su rika yawon kiwo da ke kawo rashin jituwa tsakanin su da manoma da shanun su ke lalata amfanin gonar su.

Haka kuma, gwamna Masari ya ce yana goyon baya a sake tsarin raba iko tsakanin matakan gwamnati uku da suka hada da majalisar dokoki, bangaren zartarwa da bangaren shari’a zuwa kashi 100 bisa 100.

Ya ce abin da ‘yan kasa ke nufi da sauya fasalin Najeriya kenan ya na mai cewa, idan aka tashi yin hakan kamata ya yi gwamnatin tarayya ta sanya mizani ko iyaka da ba za'a ketara ba don cimma nasara.

Haka kuma, Masari ya ce "maganar sauya fasalin kasa an dade ana yin ta, tun a jamhuriya ta daya sakamakon yadda aka tattare karfin iko da yawa a tsakiya kuma 'yan kasa ba sa son a dore a hakan."

Gwamna Masari ya kuma yi misali da cewa, a yayin da jihar Legas ke samun kudaden shiga na kimanin naira biliyan 400, gwamnan Kano ma zai samu kudaden shiga da zai fi nasa a jihar Katsina wanda bai wuci biliyan biyu ba, saboda haka idan aka yi rabon ikon yadda ya dace komai zai tafi kamar yadda 'yan kasa ke muradi.

Ya ci gaba da cewa kuma dole a yi amfani da yanayin samun kudadden shiga a kayyade albashi, inda ya ce kansila a jiharsa abin da zai samu na albashi da gudanar da aiki zai kasance ne gwargwadon karfin arzikin jiharsa ba kamar na Legas ko Kano ba.

XS
SM
MD
LG