Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakin Haramta Kiwo A Kudancin Najeriya Ya Saba Doka Kuma Ba Ya Maganin Matsala - Buhari


Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari.

Karon farko shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya maida martani akan matakin da gwamnonin kudancin kasar suka dauka na haramta kiwo a jihohinsu, da cewa "ba zai magance matsalar tsaro da ake fama da ita ba, illa dai kawai yunkuri ne suke yi na nuna cewa suna da karfin iko.”

A cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce matsayar da gwamnonin kudancin Najeriya suka cimma a wani taro da suka yi a ranar 11 ga watan nan na Mayu a Asaba ta jihar Delta, ya sabawa tanade-tanaden kundin tsarin mulki na ‘yanci da walwalar ‘yan kasa, na zaunawa da gudanar da kasuwanci a ko wane sashen na kasar, ba tare da la’akari da jihar su ta asali ba.

Buhari ya zargi gwamnonin na yankin kudancin Najeriya da saka siyasa a cikin muhimmin al’amari na tsaro, yana mai cewa matakin na su ma ba ya kan doka.

Ya kara da cewa manufar gwamnonin da suka sanya hannu a wannan matsaya ta taron na Asaba, shi ne kawai siyasa da nuna karfin ikonsu.

Gwamnonin Kudancin Najeriya Sun Gudanar Da Taro A Asaba, Jihar Delta
Gwamnonin Kudancin Najeriya Sun Gudanar Da Taro A Asaba, Jihar Delta

Ya ce “hakika hakki ne na jama’ar yankin kudu da ma dukkan yankunan Najeriya, shugabanninsu da wakilansu su samar da maslaha ga duk matsalolin da suka taso dangane da shugabanci da hakki, ba wai su kauda kai kan duk wata mafita mai nauyi ba, ta hanyar haramta abu baki daya a jihohinsu.”

Shugaba Muhammadu Buhari ya ci gaba da cewa “ wannan ya nuna karara cewa babu wata maslaha ko mafita da gwamnonin suka samar a cikin matakin da suka dauka, wadda za ta warware matsalar rikici tsakanin manoma da makiyaya da ya dade yana faruwa a kasar.”

Karin bayani akan: Fulani, jihar Ondo, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Akan haka ya ce tuni da gwamnatinsa ta himmatu wajen kawo karshen rikicin tsakanin manoma da makiyaya, da kuma hare-haren ta’addanci da ake ta’allakawa da Fulani makiyaya.

Daga ciki, ya ce akwai wasu matakai da ya rattabawa hannun amincewa da su, kamar yadda Ministan aikin gona Sabo Nanono ya gabatar masa a watan Afrilun da ya gabata, tun ma kafin gwamnonin su yi taro har su dauki wannan matsaya.

Buhari ya ce tuni kuma da ya amince da wani sahihin tsari na sake farfado da huruman kiwo a jihohi, inda za’a fara da jihohin da suka tsayu bil hakki kan tafarkin samar da maslaha, suke kuma iya cika sharudan da ake bukata na yin haka.

Ya ce idan aka samar da asibitocin dabbobi da wuraren shan ruwansu, da kuma ababen more rayuwa ga makiyaya da iyalansu a wadannan huruman da za’a farfado da su, hakan zai samar da gagarumin sauyi a aikace, ta hanyar baiwa al’ummomi mabambanta damar zamantakewa da taimakekeniya da juna.

Wannan ne karo na farko da shugaba Buhari ya maida martani akan matakin na gwamnonin yankin kudu da suka dauka a taron na su na Asaba makwanni biyu da suka gabata, duk da yake a makon jiya, Ministan shari’a Abubakar Malami ya fito karara ya soki matakin nasu, yana mai cewa ya saba tanade-tanaden tsarin mulki.

Malami ya kwatanta haramta kiwo a jihohin kudancin Najeriya tamkar “haramta sayar da kayan gyaran motoci a Arewacin kasar.”

ABUJA: Abubakar Malami ministan shari'a na Najeriya kuma antoni janar
ABUJA: Abubakar Malami ministan shari'a na Najeriya kuma antoni janar

To sai dai kalaman na ministan sun janyo martani da dama, musamman daga masu goyon bayan matakin gwamnonin na kudu, wadanda suka ce akwai bambanci tsakanin ayukan makiyaya a kudu da na masu sayar da kayan gyaran motoci a Arewa, kamar yadda Ministan ya ba da misali.

Shugaban kungiyar gwamnonin kudu kuma gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya kwatanta matsayin da ministan shari’a Malami ya dauka kan dokar hana kiwo a fili a matsayin "muguwar dabi’a da girman kai."

Haka ma wasu manyan lauyoyi, da mai bankin Stanbic IBTC da gidauniyar ANAP, Mr Atedo Peterside, duk sun soki minista Malami kan kalamansa.

Kungiya mai kula da muradun yarbawa zalla ta Najeriya wato Afenifere, da kakakin majalisar dattawan Najeriya, sun yi kira ga shugaba Buhari da ya cire Malami kan mukamin sa sakamakon kalmomin sa kan harmata kiwo barkatai da gwamnonin kudu suka yi, suna cewa, wadanda ke kushe haramcin na son a cigaba da kashe-kashe ne.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG