Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Matasan Fulani Ta Soki Matakin Hana Kiwo A Fili A Kudancin Najeriya


Wani makiyayi yana kiwon dabbobinsa a yankin jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya
Wani makiyayi yana kiwon dabbobinsa a yankin jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya

Kungiyar matasa Fulani ta Jode Jam Fulani Youth Association of Najeriya, ta bayyana rashin amincewarta da matakin hana kiwo a fili da gwamnonin kudancin Najeriya suka ayyana a garin Asaba, babban birnin jihar Delta a kwanan nan.

A baya-bayan nan ne kungiyar gwamnonin shiyyar kudancin Najeriya suka ayyana hana kiwon dabbobi a fili a garin Asaba babban birnin jihar Delta.

Lamarin da ke fuskantar suka musamman daga kungiyoyin Fulani na Najeriya, ganin cewa hakan a cewarsu, ya sabawa ‘yancin makiyaya a kasar.

Shugaban kungiyar Fulani ta Jode Jam, Mallam Sa’idu Mai Kano, ya bayyana wannan doka a matsayin wadda ba za ta tabbatar da zaman lafiya a Najeriya ba, ganin cewa abin da wasu Fulani suka gada kenan kuma ita ce sana’arsu.

Mallam Sa’idu ya yi kira ga shugaban kasa da ya duba wannan lamari domin hanya ce da aka dauko ta wargaza zaman lafiya a kasa.

Samun matsala tsakanin manoma da makiyaya lamari ne da ya dade ana fama da shi tare da neman mafita a kasashen yammacin nahiyar Afirka.

Shugaban kungiyar Fulani makiyaya MACBAN, Alhaji Gidado Saddiq, na ganin an dauki wannan mataki ne biyo-bayan matsin lamba daga al’umomin yankin kudu.

Sai dai an bar baya da kura ganin cewa babu wani tanadi da aka yi wa su makiyaya.

Haka kuma Gidado ya yi kira ga samar da mafita ta hanyar zama tsakanin Bangarorin biyu domin fahimtar yadda za a tabbatar da cewa ba a take hakkin wani dan Najeriya ba.

Domin karin bayani saurari rahotan Alphonsus Okoroigwe.


XS
SM
MD
LG