Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Sun Ce Arewacin Nijeriya Na Iya Dogaro Da Noma


Noma Tushen Arziki kuma maganin yunwa
Noma Tushen Arziki kuma maganin yunwa

Kwararru sun lura cewa noma na iya kai arewacin Nijeriya ga gaci. To amma ana sako sako da bangaren na noma.

Mahalarta bikin nuna amfanin gona na jihar Kano ta arewacin Nijeriya sun lura cewa, arewacin Nijeriya na iya dogaro da noma don rayuwa kamar kowane bangare amma kamar ba a sanda da hakan ba.

Bikin, wanda ya tara masana daga sassa daban daban da kuma fannoni daban daban na kimiyyar noma, sun ce ya zama wajibi ga bangaren arewa, ba ma Kano kawai ba, ya ba da himma sosai wajen habbaka bangaren noma.

Kwamishiniyar Ma’aikatar Gona ta jihar Kano Dr. Baraka Sani ta bayyana wa wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari

cewa makasudin bikin shi ne a hada masana a kimiyyar noma da sauran dabarun noma su yi musayar ra’ayi kan hanyoyi daban daban na inganta noma a arewacin Nijeriya kuma musamman ma a jihar Kano. Ta ce bikin na kuma da zummar baje kolin wasu kayan aikin noman zamani da kuma dabarun zamani.

Shi ma Ciyaman din Kwamitin Ayyukan Noma na Majalisar Dokokin jihar ta Kano Alhaji Abdullahi Mohammed Isyaku y ace Majalisar ba ta wasa da duk wani mataki na inganta noma a jihar Kano da ma arewacin Nijeriya baki daya. Y ace fannin noma na daya daga cikin fannonin da ke da kaso mai yawa a kasafin kudi kuma hakan zai cigaba da kasancewa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG