A cikin hirarsu da wakilin Sashen Hausa Ladan Ibrahim Ayawa, kakakin kungiyar Alhaji Mohammed Tukur yace ba batun sayen motocin sulke da ma’aikatar tayi kadai ne ya tada masu da hankali ba, amma da batun kara yawan haraji da kuma wadansu albazaranci da ake yi a ma’aikatar ba tare da an yi wani abin azo a gani na inganta harkokin sufufin jiragen sama a kasar ba. Alhaji Tukur yace banda kwaskwarima da ake yiwa wadansu tashoshin jiragen saman kasar, babu wani abinda ake yi na inganta ayyukan sufurin jiragen sama kamar sauka da tashin jiragen.
Sai dai da yake maida martani, kakakin harkokin sufurin jiragen saman na Najeriya Yakubu Datti yace babu kanshin gaskiya a zargin na Alhaji Mohammed Tukur wanda ya bayyana a matsayin dan karen farautar masu sufurin jiragen saman. Ya kuma musanta cewa ana kara masu ba gaira ba dalili.
Ga cikakken rahoton