'Yan haramtacen kungiyar Yarbawa zalla wato OPC sun yi hargowa gaban cibiyar harkokin kasa da kasa lokacin da aka hana su shiga harabar kwamitin dake baiwa shugaban kasa shawara kan taron kasa.
Yayin da aka bari suka shiga sai daya daga cikinsu ya yiwa taron jama'a dake waje jawabi yana cewa yana fata ba za'a jefar da bukatun jama'a ba. Ya ce idan an yi hakan ana nufin neman tada zaune tsaye ke nan. Ya ce tun tuni yakamata ayi taron don haka sun zo ne su bayyana nasu ra'ayin. Ya ce suna son su Yarbawa a bar su fice daga tarayyar Najeriya domin babu tabbas samun cigaba a tarayyar. Yarbawa na neman tasu jamhuriyar kuma kowa ya kama gabansa. Ya sake cewa babu alamun wani cigaba ma Yarbawa a Najeriya. Kana ya kira Jonathan ya tabbatar bai yiwa sakamakon taron jifar mataccen mage ba.
Kusan duk wadanda suka yi magana a taron bakinsu ya zo daya. Wasu sun ce a raba kasar kowace kabila ta kama gabanta. Wasu sun ce a koma irin shiri na da , wato shiya-shiya. Wasu kuma cewa suka yi taron na bukatar duk kabilun Najeriya su samu wakilci a cikinsa. Wasu kuma sun yi kashedin kada gwamnati ta samu wakilci a taron. Sun kuma kira 'yan majalisun kasar su tanadar da dokar da zata baiwa taron 'yancin cin gashin kansa ba sai an kare ba abun ya koma tatsuniya.
Amma kungiyar masu rashin aikin yi sun ce rashin aikin yi ya sa sun yiwa kwamitin tanadin dalilai 25 da suke gani suna da mahimmanci. Cikin wasu abubuwan da suka ce shi ne baiwa kananan hukumomi mallakar cikin gashin kansu, da samun filaye a saukake. Game da batun tsarin dan kasa sun ce duk inda mutum yake nan ne jiharshi. Kan barayin mai sun ce a yi masu hukuncin kisa.
Ga karin bayani.
LABARI: “Akwai cigaban wannan labari, da wasu labaran masu dumi-dumi, da hotuna, da bidiyo, da cikakkun shirye-shiryen mu duk a shafinmu na www.voahausa.com.”