Barrister A. T, Shehu, sakataren PDP-Tsohuwa a jihar Adamawa, ya ce ba zasu yarda da karbo wannan rancen ba, domin ko kiran jama'a su bayyana ra'ayoyinsu a kan wannan ba su yi ba.
Kakakin majalisar dokokin jihar ta Adamawa, Ahmadu Umaru, yace kalamun nan ba su dace da su fito daga bakin wanda kansa ya waye ya san al'amuran duniya ba, domin ba wai an kafa majalisa ce domin ta yakio shugaba ko gwamna ba,s ai don ta yi dokar da a ganinta ta dace.
Darektan yada labarai na gwamna Murtala Nyako, Alhaji Ahmed Sajo, yace jahilci ne ma yasa aka kasa fahimtar musabbabin karbo wannan rancen, domin mataimakin shugaban Najeriya, Namadi Sambo, shi ya kulla yarjejeniyar karbar wannan bashi daga hannun bankin, kuma daga ciki aka gutsura ma jihar Adamawa wani kaso.
Ibrahim Abdulaziz yana tafe da cikakken bayani
LABARI: “Akwai cigaban wannan labari, da wasu labaran masu dumi-dumi, da hotuna, da bidiyo, da cikakkun shirye-shiryen mu duk a shafinmu na www.voahausa.com.”