A cikin 'yan kwanakin nan rahotani suka yi ta bazuwa a tsakanin alhazan jihar dake Makka a yanzu cewa wani bam ya tashi a filin jirgin saman Maiduguri lokacin da wani jirgi ke sauka da lahazai, kuma a dalilin haka an dakatar da aikin kwasarsu.
A lokacin da yake karyata wannan labarin, Amirul Hajj kuma mataimakin gwamnan Jihar Borno, Alhaji Zanna Umar Mustafa, yace a idonsa jirage na biyu da na uku suka sauka a Maiduguri, kuma a yanzu haka an shafe watani da dama ko harbin bindiga ba a samu a Maiduguri ba, balle kuma tashin bam.
Amirul Hajjin yace babu wata matsalar tsaro da ake fuskanta da zata shafi aikin kwaso alhazan, ya kuma roki jama'a da su guji yada irin wannan jita-jita maras tushe.
Sa'adatu Mohammed Fawu na tafe da cikakken bayani.