Jami’ai suka ce an kama wadannan mutane masu niyyar zamowa bakin haure yau asabar cikin wasu motoci biyar a lokacin da suka bar garin Arlit na arewacin kasar.
Shugaban wata kungiya mai zaman kanta a Arlit yace hukumomi sun saki mutanen da ‘yan garin Arlit ne a cikin wannan tawaga.
A cikin wata hirar da yayi da Muryar Amurka, Moustapha Alhacen yace sauran mutanen da suka fito daga wasu garuruwa a cikin jamhuriyar Nijar an tasa keyarsu zuwa garuruwansu. Yace wasu kuma daga Najeriya makwabciyar Nijar suke, kuma hukumomi su na shirya yadda zasu mayarda su gidajensu.
Kamfanin dillancin labaran Faransa yace akasarin mutanen mazaje ne, amma kuma akwai yara a cikinsu.
Jamhuriyar Nijar tana tsakiyar hanyar da baki ke bi daga kasashen kudu da hamadar Sahara zuwa Turai.
Wannan ala’amarin yana faruwa ne ‘yan kwanaki kadan a bayan da hukumomi suka gano gawarwakin da suka fara rubewa na wasu bakin haure su 92 wadanda kishin ruwa ya kashe su a lokacin da suka yi kokarin ketare hamadar Sahara. Akasarinsu mata ne da yara kanana.