Dr Ahmad yace siyasar hamayya wani ci gaba ne mai kyau kuma abu ne da ake bukata a kowacce damokaradiya, sai dai matakan da yan sabuwar jam’iyar ta APC ke dauka da kuma yadda sauke yi, ya nuna sai kace akwai wata jikakkiya tsakanin wadansu da wadansu, wanda yana iya zama cikas a cikin al’amarin.
Bisa ga cewar Dr Sa’idu, hanyar da suka bi suka ta zuwa wajen gwamnoni dake bisa mulki suka yi watsi da gwamnonin da suka sauka ya nuna sai kace akwai wata jikakkiya tsakanin wadansu ‘yan APC din da wadansu, wanda ba zai haifarwa da APC alheri ba. Yace idan aka tafi haka ba a gyara ba, zai zama sai kace ka toshe kofa daya ka balle daya.
Yace da akwai ci gaban da ake dashi kamar yadda ake yi a Amurka da sauran manyan kasashe inda ake iya amfani da alkaluma na yin bincike a gano yadda daukar mataki kaza zai sa ka cimma buri kaza kayi asarar kaza, da suna da irin wannan, da zasu iya sanin ko matakan da suke dauka zasu kaisu ga cimma nasara ko babu. Amma da yake babu irin wannan damar binciken, kaiwa wadansu ziyara da kuma kaucewa wadansu wadanda sune ‘ya’yan jam’iya yana iya zama da hatsari ga jam’iyar domin wadanda ake zawarcinsu sababbi ne wadanda babu tabbacin zasu amsa gayyatar ko ba zasu amsa ba.
Ga cikakkiyar hirar.