Majalisar ta fara shirin samarda dokar haramtawa Fulami makiyaya rike duk wani makami irin su adda da bindigogi har da sanda a duk fadin jihar.
Majalisar tace ta dauki matakin ne domin kawo karshen hare-haren da Fulani ke kaiwa jama'a da zara wata matsala ta samu.
Amma a bangaren Fulani shugabanninsu sun ce hakan ba zata sabu ba.
Onarebul Bello Agwara shugaban marasa rinjaye na majalisar ya yi karin haske akan matakin da majalisar ta dauka. Yace sun gano cewa da zara akwai 'yar matsala tsakanin makiyayi da wani sai ya zaro makami ya yi anfani dashi. Idan adda ce sai ya yi sari da ita idan kuma bindiga ce ya yi harbi da ita.
Mataimakin shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah a Najeriya Alhaji Usaini Boso yace ba zasu amince da dokar ba. Yace idan zasu yi doka su yi akan kowa akan rike makami. Amma rike adda da sanda abun gado ne ga Fulani domin ado da kariya.
Shi ma sakataren kungiyar Fulanin Abubakar Sadiq yace matsayin 'yan majalisar abun takaici ne saboda Fulani suna da matsaloli musamman abun da ya shafi sace masu dabbobi. Bugu da kari majalisar bata taba yin magana akan burtulolinsu da makarantunsu da muhallansu ba, sai kawai a ce za'a yi doka akan kabila Fulani.
Duka shugabannin Fulani sun yi watsi da dokar. Sarkin Fulanin Chanchaga Alhaji Abdullahi Adamu Babayo yace matakin da majalisar take son ta dauka zai tauyewa Fulani hakinsu ne. Yace bata yiwuwa a ce mutum na cikin daji ba zai rike adda ko sanda ba.
Ga karin bayani.