A yau Litinin Majalisar Dokokin Amurka ta tabbatar da nasarar da Donald Trump ya samu a zaben shugaban Amurka a kan mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris.
Mataimakiyar shugaban kasa, Kamala Harris ce tantance sakamakon zaben da aka samu jihohin Amurka 50,
Hakan na nufin Kamala Harris ta tantance rashin nasarar da ta samu a zaben da aka gudanar a Nuwamban 2025.
Aikin tantance kuri’un wata dadaddiyar al’ada ce a siyasar Amurka, sai dai shekaru 4 da suka gabata ta rikide zuwa hargitsi bayan da magoya bayan Donald Trump suka yiwa ginin Majalisar Dokokin kasar tsinke, inda suka raunata kimanin jami’an ‘yan sanda 140, tare da lalata ginin da tursasawa ‘yan majalisar gudun neman tsira.
Ba a hasashen samun makamancin wannan yanayi a yau Litinin, kasancewar Kamala Harris ta amince da shan kaye kuma Shugaba Joe Biden ya bukaci a gudanar da aikin tantance sakamakon zaben cikin lumana.
Hukumomin tsaro sun kasance cikin shirin ko ta kwana, inda suka giggitta shingen karfe a kewayen ginin majalisar.
Dandalin Mu Tattauna