Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya Taya Trump Murnar Sake Zabensa


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya shiga sahum sauran Shugabannin duniya wajen taya Trump murnar sake zabensa a matsayin Shugaban kasar Amurka na 47.

A cikin wata sanarwa da ke dauke da sa hannun mai ba Shugaba Tinubu shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Ona¬nuga, Tinubu ya bayyana cewa, yana fatan karfafa dankon alakar Najeriya da Amurka “a daidai lokacin da ake fuskantar kalubale a kasashen duniya, da kuma damamaki a wani gefen a zamanin yanzu”.

Shugaban Najeriya ya kara da cewa Trump "zai wanzar da zaman lafiya a duniya.".

harris-ta-kira-domin-taya-trump-murnar-cin-zabe

Ya kuma kara da cewa, zasu hada hannu wajen bunkasa Najeriya. Yace, "Tare, za mu iya hakaka hadin gwiwar tattalin arziki, inganta zaman lafiya, da magance kalubalen duniya da suka shafi 'yan kasarmu.

"Nasarar da Trump ya samu na nuna amana da amincewar da jama'ar Amurka suka ba shi a shugabancinsa," in ji shi.

Donald Trump
Donald Trump

Shugaba Tinubu ya kuma taya Amurkawa murna kan jajircewarsu a fannin damokaradiyya.

Tun farko shugabannin kasashen Duniya sun aika da sakonni taya murna ga Shugaba Trump.

Zaben fitar da gwani na masu kada kuri'a a ranar Talata ya nuna cewa ya lashe zaben sabon wa'adin mulki ta hanyar lashe mafi yawan kuri'un maza da farar fata da su je jami'a ba, yayin da masu zabe da bisa al'ada su ke zaben jam'iyyar Democrat, 'yan Latino da kuma matasa suka jefa masa kuri'a.

Trump ya kwato a kalla hudu daga cikin jihohin da ya sha kaye a hannun Biden a shekarar 2020: Georgia, Pennsylvania, Michigan da Wisconsin. Kawo yanzu ba a sanar da sakamakon zaben wasu manyan jihohi biyu ba - Arizona da Nevada.

Trump da Vance za su shiga ofis tare da rinjayen Republican a Majalisar dattijai, ko da yake ba a tabbatar da jam'iyar da za ta sami rinjaye a Majalisar wakilai ba jiya Laraba.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG