Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Duniya Sun Taya Trump Murnar Nasarar Cin Zabe


Shugabannin duniya sun taya Donald Trump murnar lashe zabe bayan da hasashen kafafen yada labarai ya nuna cewar ya samu kyakkyawan rinjaye a zaben shugaban Amurka na bana.

Trump ya samu galaba a kan abokiyar hamayyarsa ta jam'iyyar Democrat Kamala Harris, abin da ya baiwa tsohon shugaban kasar jam'iyyar Republican din damar kafa gagarumin tarihin yin kome bayan shafe shekaru 4 ba a kan karaga ba.

Tunda sanyin safiyar yau Laraba, shugabannin duniya da dama suka hau kan shafukan sada zumunta na X wajen taya Trump murna, wanda tsarin hulda da kasashen ketarensa da ba'a taba ganin irinsa ba mai taken "Amurka ce a gaba" ya rikita alaka da kawaye da abokan gabar Amurka da dama a wa'adin mulkinsa na farko.

Firai Ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu na daga cikin na gaba-gaba wajen aikewa da sakon taya goyon baya da jinjina ga kafa "tarihin da Trump ya yi na sake dawowa kan karagar mulki," wanda yace wata dama ce ta sake jaddada kwakkwarar alakar dake tsakanin Isra'ila da Amurka.

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky wanda ya bukaci samun karin goyon bayan Amurka da kasashen yammacin duniya wajen yaki da mamayar Rasha, ya bayyana jin dadinsa game da abinda ya kira da jajircewar Trump wajen wanzar da zaman lafiya ta hanyar amfani da karfi a lamuran duniya.

"Wannan shine hakikanin akidar da za ta gurguso da zaman lafiya a Ukraine a zahiri. Ina fatan zamu aiwatar da hakan a tare kuma a aikace," a cewar Zelensky.

Shugaban kungiyar NATO-rundunar tsaro ta kasashen yamma da Trump ya jima yana suka a kan rashin taka rawar da ta dace wajen tabbatar da tsaron nahiyar Turai, shima ya yi makamantan wadannan kalamai a sakon taya Trump murna.

Yace "Shugabancinsa zai kasance mai mahimmanci wajen karfafa kawancenmu. Ina sa ran sake yin aiki tare da shi wajen wanzar da zaman lafiya ta hanyar karfi ta hanyar #NATO", a cewar Mark Rutte, Babban Sakataren NATO.

Shima Shugaban Faransa Emmanuel Macron na cikin wadanda suka yi gaggawar tura sakon taya murnarsu, inda yace a shirye muke aiki tare kamar yadda muka yi tsawon shekaru 4 a bisa amincewarka da tawa."

Firai Ministan Burtaniya Keir Starmer yace gwamnatinsa za ta tsaya kafada da kafada wajen kare muradan da mukayi tarayya akai na 'yanci da dimokiradiya da cinikayya.

Ursula Von Der Leyen, Shugabar Tarayya Turai, tace tana matukar taya Trump murna tare da yin jinjina ga alakar dake tsakanin tarayyar Turai da Amurka.

A lokacin wa'adin mulkin Trump na farko an samu takun saka tsakanin tarayyar Turan da Amurka, a kan kakaba haraji a kan kayayyakin da ake fitarwa daga Turai.

Suma shugabannin nahiyar Asiya sun fara aikewa da sakonnin taya murnarsu.

Firai Ministan Austireliya Anthony Albanese yace, "al'ummar Austireliya da na Amurka manyan aminai ne kuma abokan kawance na gaskiya."

Firai Ministan Indiya Narendra Modi ya mika sakon taya murnarsa ga trump, wanda ya bayyana da abokinsa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG