Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Ya Lashe Zaben Shugaban Amurka Na 2024


Wannan nasara ta Trump ta biyo bayan gagarumin zabe wanda ya kawo tsauri sosai tsakanin jam’iyyun siyasa da kuma yankunan Amurka.

An sake zaben tsohon shugaban Amurka Donald Trump a matsayin shugaban kasar Amurka a zaben 2024, wanda ya yi nasara a kan mataimakiyar shugaban kasa, Kamala Harris.

Wannan nasara ta Trump ta biyo bayan gagarumin zabe wanda ya kawo tsauri sosai tsakanin jam’iyyun siyasa da kuma yankunan Amurka.

Sakamakon zaben da aka gudanar ya nuna yadda Trump ya samu kuri’un da suka kai shi hanyar lashe zaben tare da samun rinjayen wakilan zabe na shugaban Kasa (Electoral College).

Wannan nasara ta kuma fito fili ne daga kuri’un wasu muhimman jihohin da aka sa ido sosai a kansu. Jim kadan bayan ayyana sakamakon, Trump ya gode wa magoya bayansa a wani jawabi da ya gabatar, yana mai cewa "Amurka ta bamu wata babbar dama da ba a taba ganin irinta ba.”

Sakamakon wannan zabe zai ci gaba da jan hankali musamman ganin yadda ya kawo wani sabon shafi a tarihin siyasar Amurka, inda Trump zai zama daya daga cikin tsoffin shugabannin kasa da suka sake komawa kan mulki bayan shekaru hudu.

Wannan zabe na shekarar 2024 ya kuma janyo hankalin duniya saboda zai iya kawo sauye-sauye a manufofin Amurka a fannonin tattalin arziki da shige da fice da tsaro da kuma dangantakar Amurka da sauran kasashen waje.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG