Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harris Ta Kira Domin Taya Trump Murnar Cin Zabe

A yau Laraba Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris ta kira Donald Trump domin taya shi murnar cin zaben shugaban kasa na bana, a cewar daya daga cikin hadimanta, bayan zazzafar takarar da suka yi.

Harris 'yar jam'iyyar Democrat ta tattauna da Trump a kan mahimmancin mika mulki cikin lumana da zama shugaban kasar dukkanin Amurkawa, a cewar hadimin dake bayani a madadinta.

Daga bisani Harris ta gabatar da jawabin amincewa da shan kaye a hannun abokin hamayyarta na jam'iyyar Republican kuma zabebban shugaban kasa Donald Trump.

Da safiyar yau Laraba Trump ya lashe zaben shugaban kasar Amurka bayan da ya samu kuri'un wakilai 292 daga cikin 538.

A halin yanzu harris tana da kuri'un wakilai 224.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG