Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Ake Gudanar Da Zaben Sabon Shugaban Kasar Amurka


US-VOTE-POLITICS-ELECTION
US-VOTE-POLITICS-ELECTION

Masu zabe a Amurka zasu yanke hukunci a yau bayan wani zabe mai cike da sammatsi da ka iya mayar da Kamala Harris ta zamo shugabar Amurka mace ta farko a tarihi ko kuma ya baiwa Donald Trump damar yin kome abin da ke razana duniya.

A yayin da aka bude rumfunan zabe a fadin Amurka a ranar zabe, ‘yar takarar jam’iyyar Democrat mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris, mai shekaru 60 da dan takarar jam’iyyar Republican tsohon shugaban kasa Donald Trump, mai shekaru 78, sun yi kankankan a takarar shugaban Amurka mafi rashin tabbas a zamanin da muke ciki.

Abokan hamayyar sun shafe ranaikun karshe na yakin neman zabensu suna kokarin yiwa magoya bayansu kaimi domin su fito su yi zabe tare da kokarin shawo kan duk mai niyar zaben da bai yanke dan takarar da zai zaba ba a jihohin rabagardamar da ake sa ran zasu sauya alkaluman zaben.

An bude rumfunan zabe da msalin karfe 6 na safe a jihohin dake gabar gabashin Amurka kuma ana sa ran milyoyin masu zabe su kada kuri’unsu, kari akan fiye da mutum milyan 82 da suka riga suka yi zabe a makonnin da suka gabata.

Za’a shafe kwanaki kafin sanin sakamakon karshe idan har aka yi kankankan kamar yadda zaben ke nunawa, inda yake kara zaman dardar a kasar dake fama da rabuwar kannu.

Wakilan Muryar na dauke da karin bayani kamar yadda za ku ji a sauti

Hira Da Ibrahim Garba Kan Yadda Aka Tsara Gudanar Da Zabe A Gundumar Kwalambiya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Hira Da Mahmud Lalo Kan Yadda Aka Tsara Gudanar Da Zabe A Jihar Virginia
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00
Hira Da Sarfilu Hashim Kan Yadda Aka Tsara Gudanar Da Zabe A Jihar Maryland
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:16 0:00

Sai dai jami'an tsaro sun kori 'yan jarida da suka halarci Martin Luther Memorial Library domin ganin irin wainar da ake toyawa dangane da zabe a wajen.

ZABEN AMURKA: Yadda Jami'an Tsaro Suka Kori 'Yan Jarida Daga Martin Luther Memorial Library
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:13 0:00

Waye Ya Cancanci Kada Kuri'a?

Domin kada kuri'a a zaben shugaban Amurka, wajibi ne wanda zai kada kuri'ar ya kasance dan asalin Amurka, kuma shekarunsa na haihuwa sun cika 18 a ranar zaben ko kafin lokacin kuma ya cika sharuddan zaman wuri, wadanda ke bambanta daga jiha zuwa wata jihar.

Haka kuma wajibi ne masu niyar kada kuri'a suyi rijista a bisa dacewa da wa'adin rijistar zaben jihohi. Wasu jihohinma suna takaita kada kuri'a ga fursunonin da aka yankewa hukunci akan manyan laifuffuka ko mutanen dake larurar tabin hankali.

Gaba daya, Amurkawan dake zaune a wajen kasar na iya zabe ta hanyar kuri'ar nesa, sai dai a zaben shugaban kasa, Amurkawan dake zaune a yankunan da Amurka ke iko dasu, ciki har da Puerto Rico, Tsibirin Virgin, Tsibirin Arewacin Marianas da kuma Samoa ba za su iya yin zabe ba.

Shin ya ya ake kirga kuri'u?

Amurka ba ta da babbar hukumar zabe. Kowace jiha kan shirya irin tsarinta na kirga kuri’u.

Jami’an jihohi dana kananan hukumomi suna bada rahoton sakamakon zabe nan take, su kuma kafafen yada labarai sai suyi amfani da sakamakon, a akasarin lokaci da bayanan alkaluma, domin fayyace wanda ya lashe zaben.

Sau da yawa kafafen yada labarai kan sanar da wanda ya lashe zabe kafin kammala kidayar kuri’u ko jami’ai su sanarda sakamakon.

Dalili kuwa shine a kan dauki kwanaki ko makonni kafin a kammala kidayar kuri’u a gundumomi haka kuma sau da yawa, wani sashi na sakamakon ya wadatar a iya tantance wanda ya lashe zaben a lissafe.

Sai dai, duk lokacin da aka yi kankankan, kafafen yada labarai kan tsahirta wajen ayyana wanda ya lashe zaben har sai an bada sakamakon karshe.

Ba a fara bada rahoton sakamakon farko har sai an rufe rumfunan zabe a hukumance.

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump bayan ya kada kuri'arsa a birnin Palm Beach na jihar Florida.

A saurari rahoton da wakilin Muryar Amurka, Mahmud Lalo, ya hado mana kan yadda zaben ya gudana a jihar Virginia.

Yadda Aka Gudanar Da Zaben Shugaban Amurka A Jihar Virginia
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG