Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatar Shari'ar Amurka Ta Bukaci Kotun Koli Ta Soke Hukuncin Kotun Tarayya


Wata kotun tarayya ta tsame kakannin mutanen da ke zaune a Amurka, daga cikin jerin mutanen da doka ta hana shigowa Amurka.

Ma'aikatar Shari'ar Amurka na bukatar Kotun Koli ta soke hukuncin wani alkalin kotun Tarayya, wanda ya tsame kakannin mutanen da ke zaune a Amurka, daga cikin jerin mutanen da dokar hana shigowa ta Shugaba Donald Trump ta shafa.

Ma'aikatar ta Shari'a ta gabatar da bukatar a gaggauce da daren jiya Jumma'a.

Ranar Alhamis wani alkalin kotun gunduma a Honolulu mai suna Derrick Watson ya yi kiran da a rinka amfani da abinda ya kira "hankali" yayin da ya ke kara nau'ukan 'yan uwan mutanen da ke zauna a Amurka da ka iya shigowa daga kasashe 6 masu rinjayen Musulmi - wato Iran da Libiya da Somaliya da Sudan da Siriya da Yemen.

Watson ya umurci gwamnati da kar ta aiwatar da dokar kan kakanni, da jikoki da kuma surukai da goggonni da kawunnan mutanen da ke zaune a Amurka.

Watson ya kuma zartas cewa duk wani dan gudun hijirar da wata cibiyar tsugunar da 'yan gudun hijira ta yi alkawarin daukar nauyinsa a Amurka a bar shi ya shigo.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG